Harin sojin Najeriya ya halaka matar Shekau
October 25, 2017A cewar rundunar a makon da ya gabata ta kai wani hari ta sama kan mayakan a yayin da suke ganawa a wani gari da ke yankin Konduga na jahar Borno. Sanarwar ta kara da cewa harin ya halaka mayakan kungiyar da dama tare da haifar da gobara.
Kakakin sojan saman kasar Olatokunbo Adesanya ya ce, su na kokarin sanin ko wata mata mai suna Firdausi da ke cikin wadanda harin ya halaka lallai mai dakin shugaban kungiyar ta Boko Haramun ce.
Adesanya ya ce, bayanan da suka samu ya nuna cewa, Firdausi ta maye gurbin mijinta inda ta ke wakiltar Shekau a duk wani taro da mayakan da ke biyayya ga shugaban kungiyar da ayyukanta ya haifar da asarar rayukan mutane da dama a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya.Ana kyautata zaton su na cikin irin wannan zama a lokacin da sojojin na Najeriya suka afka musu.