Matashin da ya samar da injin janareta
July 22, 2020Matashin mai suna Abubakar Bala ya ce ya lura da yadda ake da karancin wutar lantarki da kuma tsadar man fetur a Najeriya musamman a jiharsa ta Bauchi, hakan ta sanya ya fara tunanin yadda za ayi ya kirkiri wani injin janareta wanda ba sai da albarkatun man fetur zai yi aiki ba. A cewarsa matsalar tashin farashin man fetur a Najeriya, ba abu ne da ake ganin za a iya samun saukinta nan kusa ba, don haka ne ma ya hada wannan janareta wanda ya yi amfani da kacar keke da wasu karafa wajen hada shi. Duk da yake ba wannan janareta ne inji na farko da matashin ya taba kirkira ba, amma kuma a wannan bangare na injin da baya amfani da mai shi ne na farko da ya yi, wanda hakan yasa ya zo masa da kalubale kamar na yadda injin zai fara aiki da kansa.
Dukkan wani abu na fasaha ana fatan idan anyi shi nan gaba ya zama an inganta shi yadda zai zama yafi yadda aka fara shi nagarta, domin jama'a masu bukata su aminta da amfani da shi, wannan kuma shi ne yazo daidai da tunanin Abubakar Bala inda shi ma yake da wannan buri ta inda nan gaba shi ma zai fara hada su da yawa, ganin cewa a yanzu wanda ya hada din ma jama'a na ta rububin mallakarsa. Sai dai matashin ya koka da karancin jari a hanunsa wanda zai taimaka masa wajan sayo kayayyakin aiki masu nagarta da nan gaba zai samu damar hada injin janaretan da suka fi wanda ya hada a yanzu.