1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai zana injina a Kano

May 19, 2021

Shi dai wannan matashi na ya ce ya koyi zane tun yana makaranta, inda daga bisani ya ce ya fadada bincike har ya bunkasa zane-zanen nasa.

https://p.dw.com/p/3tcdw
Symbolbild Cyberkriminalität
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Armer

Abubakar Buwayi matashi ne wanda bayan kammala karatun sa na ilmi mai zurfi ya kama sana'ar  zanen bangarori dabam-dabam na mota. Yakan fasalta kowane bangare na ciki da wajen mota. Wannan matashi kan yi aikin zane-zanen motocin da ya runguma a matsayin sana'a, inda yake zana duk wani injin ko na'urar da aka nuna masa daga kwamfuta.

Sana'ar Abubakar Shehu Ahmad ta bunkasa inda yake koyar da mutane da dama aikin zane-zanen motoci da injina a Kano. Ya ma taba shiga takarar mukamin kwararren masanin fasalta mota na kungiyar masana fasalin motoci ta Najeriya.