1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashin da ya kirkiro radiyo a Kano

September 22, 2021

Wani matashi a jihar Kano da ke Tarayyar Najeriya, ya kirkiri radiyo bayan da ya kammala karatunsa na diploma.

https://p.dw.com/p/40fs6
Symbolbild Radiogerät, Stereoreceiver
A jihar KAno matashi ya kirkiri radiyoHoto: picture-alliance/Klaus Ohlenschläger

Matashin mai suna Salim Haruna Bichi hazikin matashi ne da yake da matukar sha'awar kere-keren na'urori, dabam-dabam tun lokacin kuruciya. Saboda wannan sha'awa ta kere-kere da yake da ita, ya karanta darasin injiniya domin ya kara fadada baiwarsa. A yanzu da yake dab da kammala karatunsa na babbar diploma a kwalejin fasaha ta Kano, ya kera radio. Radiyon tasa dai, na kama tashoshin FM, inda yake nishadantar da mutane da abin da ya ce ya karanta a makaranta kuma ya yi bincike sosai kafin ya cimma wannan nasara. Matashin dai yana alfahari da wannan nasara da ya cimma, koda yake ba ya rasa kalubale.