A Kano an horsa da mata adana kayan amfanin gona
December 16, 2015Sai dai yadda ake sarrafa su da kuma rashin ajiya mai kyau suna hana mafi yawan ‘yan Najeriyar amfana daga dimbin sinadaran kare lafiya da suke da s u. A dangane da haka ne ma Kwalejin Aikin Gona ta Tarayya da ke Kano ta shirya wa matan karkara na wasu jihohin Arewacin Najeriyar wani horon sarrafa irin wadannan kayayyaki. Shi dai wannan horo na matan karkara kwalejin ta ce ta shirya shi ne don rage asara da ake ta kayan marmari da na lambu da kuma koya wa matan hanyoyi na sarrafa su don su ma su koyar kamar yadda shugaban kwalejin Farfesa Muhammad Sani Sule ke cewa:
"Mun gano cewa kusan kashi arba'in na kayan lambu da na marmari da ake yi a Najeriya su na lalacewa, wanda hakan ya na kawo karancinsu kuma karancinsu ya na da matukar matsala saboda suna daya daga cikin abubuwan da ke bayar da wasu sinadarai a cikin jiki da ake kira "Vitamins da Minerals". To idan ba wadannan, za a fuskanci matsalar yunwa da kuma karancin abinci."
Mata 60 ne aka zabo daga jihohi bakwai da kuma kungiyoyi 31 domin su koyi fasahar sarrafa wadannan kayayyaki. Madam Mercy Sarki daga jihar Kaduna ta koyawa matan fasahar sarrafa citta. Ita ma Mrs Abigail Banigbe malama ce da ta kware wajen sarrafa cittar ta fannoni daban-daban ta kuma akwai citta kala-kala da ake magani da ita. Ban da citta akwai sauran kayan marmari da suke kara lafiya da baiwa jiki kariya da matan suka koya, inda guda daga cikin matan ke cewa:
"Kamar yadda ta karantar da mu abin a rubuce to a cikin iznin Allah sai kuma ga shi mun ba ta a aikace kamar yadda abin yake. Shi ya sa mu tafi da shewa ko ba komai mun kwace dabarar bature."
Shi dai wannan horo ya zo a dai-dai lokacin da gwamnatin Najeriya ke bullo wa da mata hanyoyi daban-daban na karfafa musu guiwa a kan kananan sana'o'in dogaro da kai.