1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zabe mai kanta, ta bada sakamakon zaben shugaban kasar Cap Vert

February 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7z

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Cap Vert, ta bayyana sakamakon karshe, na zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar lahadi da ta wuce.

Shugaba Pedro Pires, yayi tazarce, tare da tattara jimmilar kashi kussan 51 bisa 100 na daukacin kuri´un da aka kada.

Babban abokin hamayar na sa Carlos Vega ya samu kashi 49 da yan ka bisa 100.

Hukumar zaben ta bayyana cewa, kussan kashi 50 ne, na mutanen da ya cencenta su ka kada kuri´a, su ka kauracewa zaben.

Cemma a zaben shekara ta 2001 wanan takara 2 su ka fafata, inda shugaba Pedro Peres ya tserawa Carlos Veiga, da kuri´u 12 rak.

Kamar kuma wacen shekara mutanen Cap Vert da ke zaune a kasashen ketare su ka ba shugabandamar samun wannan nasara, ta hanyar lashe kashi 64 bisa 100 na kuri´un da a ka kada kasashen ketare.

Ta fanin kuri´un da a ka jefa ciki tsibirin dan takara day a sha kasa ke sahun gaba.