1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zaben Najeriya ta mika wuya

Uwais Abubakar Idris
February 18, 2019

A Najeriya hukumar zaben mai zaman kanta INEC, ta amince wa jam’iyyun siyasa da su ci gaba da yakin neman zabensu biyo bayan dage babban zaben kasar da ya haifar da takaddama.

https://p.dw.com/p/3DboE
Nigeria Rivers State | Wahlkampf Muhammadu Buhari, Präsident
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency/Bayo Omoboriowo

Wannan ya biyo bayan bukatar da jam’iyyun da ma sauran masu ruwa da tsaki a harkar suka ne yi a taron da hukumar zaben ta kamala a Abuja.

Hukumar zaben Najeriyar da ta kwashe lokaci mai tsawo tana taro a kan lamarin, kafin ta yanke hukuncin bai wa jam’iyyun siyasar damar ci gaba da yakin neman zaben nasu, bayan kama kafa da masu ruwa da tsaki a harakar zaben suka yi.

Kwamishinan mai kula da yada labaru da wayar da kan jama’a a kan zabe Festyus Okoye ya shaida wa DW cewar sun yi hakan ne don bin doka da bukatun al’umma musamman jam’iyyun siyasa.

Tun da fari dai jam’iyyun siyasar kasar sun dage kan cewa tunda an dage zaben, za su ci gaba da yakin neman zabe daga nan har zuwa karfe 12 na daren ranar Alhamis da ke tafe.

Jam’iyyar PDP ta hamayya, na daga cikin jam’iyyun da suka tsaya kan wannan bukata.

Ita kanta jam’iyyar APC da ke mulki a Najeriyar ta ce sake tsunduma cikin yakin neman zaben, muhimmi abu ne a gare su domin dage zaben ya sanya bata wa dumbin magoya bayansu rai, don haka zasu yi amfani da wannan dama.