1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake samun wata daga cikin 'yan matan makarantar Chibok

January 5, 2017

Sojojin Najeriya sun ceto daya daga cikin 'yan matan makarantar sakandaren Chibok da Kungiyar Boko Haram ke garkuwa da su fiye da shekaru biyu da suka gabata.

https://p.dw.com/p/2VMR3
Nigeria Afrika Soldat steht in einem Türrahmen eines zerstörten Gebäudes
Hoto: Getty Images/S.Heunis

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun sake ceto daya daga cikin 'yan matan makarantar sakandaren Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace kuma take garkuwa da su sama shekaru biyu da suka gabata.  Sojoji da matasan da ke aikin tabbatar da tsaro a shiyar arewa maso gabashin Najeriya ne suka ceto wannan yarinya a yankin Damboa da ke kusa da dajin Sambisa. Sai dai babu cikakken bayani kan yadda aka ceto yarinyar ya zuwa yanzu.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar Birgediya Janar Sani Kuka Sheka ya aike wa manema labarai, ta nunar da cewa yayin bincike 'yan matan aka ceto ta bayyana sunanta da Rakiya Abubakar. Sannan ta ce kafin sace ta ita 'yan aji uku ne na babbar makarantar sakandaren Chibok inda aka yi awon gaba da su a watan Afrilun shekara ta 2014. Sanarwar ta ce za a tantance lafiyar Rakiya kafin a mika ta ga gwamnatin Jihar Borno. Amma dai Janar Kuka Sheka ya ce tana shayar da yaro yanzu haka.