1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sallar Idi lokacin COVID-19

Abdullahi Maidawa Kurgwi LMJ
July 31, 2020

Gwamnatin jihar Filato a Najeriya, ta yaba da yadda al'ummar Musulmi suka bayar da hadin kai wajen gudanar da Sallar Idi a Masallatai na unguwanni, maimakon zuwa filayen Idi kamar yadda aka saba a shekarun baya.

https://p.dw.com/p/3gFS0
Nigeria Frauen machen einen Selfie
Mata da yara sun halarci Sallar Idin Babbar Salla a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Wani abin da DW ta lura dai shi ne yadda matan aure da dama suka samu halartar Sallar Idin Babbar Sallar ta bana, inda suka yi sahu a gefe guda. A cewar  Hajiya Zulaihat Ishaq  guda daga cikin wadanda suka halarci Sallar Idin, da ma ce ta samu gare su sakamakon  COVID-19.

A wasu Masalatan da wakilin DW ya ziyarta, ya lura da yadda al'umma suka bi ka'idojin saka tazara a sahu da kuma saka takunkumi, kana Sallar ta gudana cikin lumana da kwanciyar hankali. Hakan ce ta sanya gwamnatin jihar ta Filato ta bakin sakataren gwamnati Farfesa Danladi Atu ta yaba da dabi'ar zaman lumana na Musulmin jihar.   

Sai dai wasu magidanta ba su samu zarafin yin layya ba, sakamakon rashin kudi, duk kuwa da cewar raguna kan yi sauki bayan an sakko daga Sallar Idin.