Indiya da Canada sun sallami jakadun kasashen biyu
October 15, 2024Canada ta zargi manyan jami'an diflomasiyyar Indiya da hannu wajen kashe 'dan gwagwarmayar na Sikh, Hardeep Singh Nijjar a kasarta, zargin da Indiya ta musanta wanda kuma ke ci gaba da haifar da tsamin dangantaka.
Karin bayani: China ta zargi 'yan Kanada da leken asiri
Ko a watan Satumbar 2023, Firaministan Canada Justin Trudeau ya ce yana da hujjoji na zargin hannun Indiya dumu-dumu wajen halaka Singh Nijjar, zargin da New Delhi ke cewa bata da hannu duk da cewa Singh Nijjar 'dan ta'adda ne. An dai halaka 'dan gwagwarmayar na Sikh a birnin Surrey da ke gundumar British Columbia a kasar Canada, kuma ya kasance daya daga cikin masu gwagwarmayar yada addinin Sikh da hukumomin Indiya suka haramta a fadin kasar baki daya.
Karin bayani: Kasar Canada ta nuna damurwata ga halin kasar Mali
Indiya na zargin Canada da bai wa 'yan Sikh damar yada addininsu a kasar, wadanda kuma ke kasancewa kashi 2% bisa 100 na al'ummar kasar ta Canada da kuma ke da wakilci a majalisar dokokin kasar.