Mutum kusan dubu 80 sun kamu da COVID
August 30, 2020Rahotanni na nuni da cewar cikin tsukin sao'i 24 kacal, mutane dubu 78, 761 sun kamu da wannan cuta.
Indiya da ke da yawan al'umma biliyan1.3 dai, na zama kasa ta uku a jerin wadanda suka fi yawan masu COVID 19 bayan Amurka da Brazil, inda kawo yanzu mutane miliyan 3 da dubu 500 suka kamua kasar.
A ranar 17 ga watan Yuli ne dai, Amurka ta sanar da mafi yawan sabbin kamuwa da cutar na mutane dubu 77,638 cikin tsukin sao'i 24, a cewar alkaluman kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP.
Jamus a daya hannun Jamus nada yawan masu corona 241,771, daga cikinsu 9,295 sun rasa rayukansu.
A yanzu haka dai sama da mutane miliyan 25 ne suka kamu da cutar ta COVID 19 a fadin duniya. Tun bayan barkewar wannan annoba dai, wannan shi ne karon farko da mutane kusan dubu 80 suka harbu da cutar a rana guda.