1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC: Karuwar masu zabe a Najeriya

August 2, 2022

A wani abun da ke nuna alamun karuwar sha'awa a zabukan Najeriya na 2023, hukumar zabe ta kasar INEC ta ce an samu karuwar masu zaben da kuri'a miliyan goma sha biyu.

https://p.dw.com/p/4F2Cv
Nigeria, Wählerin mit Wählerkarte
Hoto: AFP/Getty Images/P. Utomi Ekpei

Sabuwar kiddigar hukumar zaben dai ta ce mutane kusan miliyan 100 na yan kasar ne dai ke shirin taka rawa a cikin zaben na badi.  A wani abun da ke shirin kafa tarihin zabe kuma ke kara fitowa fili da karuwar sha'awa bisa zaben da ke nuna alamun zama daban cikin kasar.

Shirin rajistar da ya faro a shekarar da ta shude ya rikide bayan zabbukan fidda gwani na takarar a matakai daban daban a cikin kasar.

Kuma jerin sha'awa kama daga batu na kabila ya zuwa ga batun addini na masu takara, ko bayan rashin tsaro, daga dukkan alamu na zaman na kan gaba wajen daukar ra'ayin miliyoyin 'yan kasar zuwa ga rajistar zaben na badi.

Auwal Ibrahim na daya daga cikin sabbin masu katin zabe a kasar da kuma yace batun tsaro na zaman na kan gaba wajen kai shi ga shafe lokaci yana layin karbar katin zaben.

To sai dai kuma idan har tsaro yana shirin tasiri a shekarar badi, banbancin addini ya hau sawun gaba tare da mayar da masallatai da mujami'u komawa fagen neman tilasta wa magoya baya samun katin.

Dr Faruk BB  Faruk mai sharhi kan siyasar da kuma yace malaman addinin na neman karbe jagorancin siyasa daga 'yan siyasar.

Ko ya zuwa ina malaman addinin ke shirin su kai cikin fatan karbe siyasar dai, rawa ta malaman addinin a fadar Reverand Joseph Hayab shugaban kungiyar kiristoci reshen jihar Kaduna, ba ta wuce neman shirya magoya baya zuwa karatun dai dai ba.