1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Barazana ga makomar zaben 2023

May 21, 2021

A yayin da ake cigaba da kona ofisoshin hukumar zabe a jihohin kudu maso gabas da kudu maso kudancin tarrayar Najeriya, hukumar zaben kasar ta INEC ta ce akwai barazana ga makomar zaben 2023.

https://p.dw.com/p/3tnSP
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Akalla ofisoshin hukumar zaben Najeriya INEC guda shida ne dai aka kona a cikin makonni biyu da suka gabata a sassan kudu maso gabas da ma kudu maso kudancin Najeriyar. Ko bayan hedikwatar hukumar ta jihar Enugu duk dai a sashen na kudu maso gabas. Abun kuma da ya tada hankalin hukumar da ta share tsawon wannan makon tana ganawa da masu ruwa da tsaki da harkar zabe a kasar.

Nigeria Regionalwahlen 2019
Wata cibiyar zabe a 2019Hoto: Reuters/A. Sotunde

A watan Juni ne dai aka tsara fara shirin babban zabe na kasar tare da bude aikin rijistar masu zabe da za ta dauki tsawo na shekara guda. To sai dai kuma ta'annatin dake zaman irinsa na farko a daukacin kasar tun bayan sake girka dimukuradiyar shekaru 20 da doriya na zaman barazana ga shirin zaben na kasa dama zaben gwamnan jihar Anambra da aka tsara gudanarwa a watan Nuwamba 2021 a fadar Nick Dazang dake zaman kakakin hukumar ta kasa.

Kundin tsarin mulki na kasar dai ya tanadi samun lashe akalla kaso daya a cikin hudu na daukacin sakamakon zabe na shugaban kasa a jihohi 24 a tarrayar Najeriyar kafin iya samun nasara a zabe na shugaban kasar. Kuma gaza zaben a jihohin 11 na yankunan guda biyu dai na iya jefa sakamakon zaben cikin rikicin dokar dake zaman mai tasiri a bisa halasci.

Duk da cewar har yanzu ana dora ayar tambaya kan masu ruwa da tsaki da kone konen dai, a fadar Dave Umahi dake zaman shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, a fasa kowa ya rasa na zaman ummul haba'isin barnar da ke iya kaiwa ga sanya  dokar tabaci a yankunan guda biyu,.

"Babban burin kona ofisoshi na hukumar INEC dai ina jin na da ruwa da tsaki da jirkita tunanin matasanmu da daman gaske game da Biafra, Biafran dake a zuciyata itace Biafra ta cigaba, Biafran da kowace jiha a kudu maso gabas za ta yi amfani da kudaden da muke samu daga tarrayar domin gina al'ummarmu, Biafran adalci a tsakanin daukacin yankunan Najeriya".

Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente
Jadawalin sunayen masu zabe a 2015Hoto: Reuters/Penney

"Ana juya tunaninsu cewar ba za'a yi zabe a cikin yankin ba, to in ance ba zabe sai majalisar tarraya ta sanya dokar ta baci a yankin, ba kuma abun da wani zai iya, saboda ba a kona ofisoshi na hukumar zabe a yankin kudu maso yamma dama ragowar yankunan kasar ba. Tunani ne maras kyawun gaske, bamu san masu aikata wannan ba amma dai mun san masu aikata laifi ne".