Takaddama kan sunaye a rajistar masu zabe
November 17, 2022Hukumar zaben Najeriya ta baje kolin sunayen mutanen da aka yi wa rajistar da yawan su ya kai milyan 93 da dubu 500. An gano kura kurai a cikin rajistar, kuma tsarin sanya hoton duk wanda ya yi rajistara shi ya taimaka aka gano haka inda aka ga sunayen yara kanana da basu kai shekaru 18 ba a cikin rajistar ciki har da jarirai baya ga wadanda suka yi rajista fiye da daya.
Wannan dai ya harzuka ‘yan siyasa da wasu matasa inda suka gudanar da zanga-zanga zuwa hedikwatar hukumar zaben.
Tuni kungiyoyin farar hula suka ce dole a sake lalle domin wannan abu ne mai hatsari sosai.
Hukumar zaben Najeriya ta ce dama manufar baje sunayen masu jefa kuri’ar an yi ne don bada damar gano kura-kurai a don a gyara.
Ko ‘yan siyasar da tuni suka fara korafi sun gamsu da alkawarin da hukumar zaben ta yi kan wannan batu?
An dai dade ana zargin amfani da yara kanana da shekarunsu bai kai su yi zabe ba, abin da hukumar zaben ta ce zai zama tarihi a bisa sabbin naurorin zamani da za ta yi amfani da su a zaben na badi domin Najeriya za ta zama abar koyi a Afrika da duniya wajen shirya sahihin zabe da zai zama karbabe ga kowa.