1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta dage shirin raba katin zabe a jihohi 8

Babangida Jibril daga MinnaNovember 28, 2014

A karo na biyu Hukumar zaben Najeriya ta dage gudanar da shirin raba katin zabe a Jihohin da suka hada da Niger da katsina da kaduna. Tuni dai 'yan Adawa suka fara zargin INEC da rawa da bazar Jam’iyyar PDP mai mulki .

https://p.dw.com/p/1Dwng
Hoto: AP

Zargin da jama'a da kuma 'yan adawa ke yi wa hukumar zaben ta INEC shi ne na rashin shiryawa, ganin yadda bayar da katin zaben na kasa ke neman ya gagari kundila, alhali watanni kasa da uku suka rage a gudanar da zaben 2015. Wani jigo a jam'iyar adawa ta APC kuma tsohon dan majalisa Hon Usman Musa kasuwan Garba ya na daya daga cikin masu zargin Hukumar ta INEC da wasa da hankalin 'yan Najeriya. Ya ce " lallai akwai lauje cikin nadi game da take- taken Hukumar INEC, domin idan har tun 2011 za'ayi katin zabe ace za'a ba dasu,a mma kuma bayarwar ta gagara , lallai akwai shakku game da shirin hukumar ta INEC.

Du kokarin jin ta bakin hukumar zaben a jihar Niger game da dage wannan rana na yin rajista da kuma bayar da katin zaben na dindindin dai ya ci tura. To sai dai a bangarensu 'ya'yan jam'iyar PDP mai mulki a Najeriya sun musanta zargin da 'yan adawa ke yi na cewar da hadin bakinsu ne hukumar ta INEC ke dage ranakun bayar da katin zaben domin samun sukunin yin magudi. A cewar daya daga cikin 'ya'yan jam'iyar a jihar Niger Malam Mohammad Mohammad ya ce "muna goyon bayan mataki dage bayar da katin ne domin mun yarda da uzurin da hukumar zaben ta bayar."

protestierende Menschen in Nigeria
APC ta yi Allah Wadai da dage shirin raba katin zabeHoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Sauran jama'a da suka yi sammako zuwa cibiyoyin zabe da nufin karbar katin nasu, sun zargi hukumar ta INEC da gazawa, tare da yaudarar jama'ar kasa game da zaben mai zuwa a shekara ta 2015. Yanzu dai hukumar zaben ta ce a farkon watan Disemba ne zata fara bayar da katin zaben a jihohi 8 da har yanzu ba su samu katin zabe ba.