1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta fitar da jaddawalin zabe na 2019

Uwais Abubakar Idris
March 10, 2017

A Najeriya, wata takadama ta kaure a game da sanar da ranakun zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokokin na Tarayya na 2019 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta yi.

https://p.dw.com/p/2Yyfd
Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hukumar zaben Najeriya ta fitar da jaddawalin zabuka na 2019Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya INEC, da ta fitar da ranakun zaben ta nuna cewa a ranar 16 ga watan Fabrairun shekara ta 2019 mai zuwa ne za'a gudanar da zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya da ya nuna kada kugen siyasa a kasar da wa'adin gwamnatin da ke mulki ke da sauran shekaru biyu.

Zargin yin riga Malam Masallaci

Wahl Nigeria Abuja
Na'urar tantance masu zabe a NajeriyaHoto: DW/Uwaisu A. Idris

Sabon salon da hukumar ta bullo da shi a cewa daga yanzu wadannan ranaku sun zauna daram ba sai kowane wa'adin mulki an yi wahalar batun tsaida ranaku na zabe ba, don ya kasance daidai da tsari. Mr Nick Dazang Daraktan yada labaru na hukumar zaben Najeriyar shi ne ya sanar da hakan. Tuni dai ‘yan siyasa suka fara sharhi da maida martani a kan wannan sabon babi na ranakun zaben a Najeriya, inda wasu ke cewa hukumar ta yi riga Malam massalaci, amma ga wasu manyan 'yan siyasan na Najeriya na masu hangen alfanu da ma muhimmancin yin hakan ga daukacin tsarin dimukurdiyyar Najeriyar.

INEC ta ce fitar da jaddawalin na cikin tsari

Nigeria, Wählerin mit Wählerkarte
Tsaida lokacin zaben da wuri zai bada damar kammala shiri kafin lokaciHoto: AFP/Getty Images/P. Utomi Ekpei

Sanin cewa a baya dai sanar da ranakun zaben na nuni da kada kugen siyasa ne na fara yakin neman zabe, abin da ke kan katse hanzarin gudanar da ayyukan gwamnatin da ke kan mulki. To sai dai daraktan hukumar zaben ta Najeriya ta ce akwai bukatar ta fahimtar lamarin, domin ba wai sun buda kofa a fara kamfe da yakin neman zabe ba ne.

Tuni dai aka fara ganin alama ta fafatawar da za'a yi a tsakanin jam'iyyu da ma ‘yan takara da suka fara kunno kai da yawansu ya kai mutane 15 da za su fafata a zaben shugaban kasar Najeriyar a 2019. Zaben da masana harkokin siyasa ke ganin cewa zai kasance mai ban sha'awa saboda kara wayewar da kan mage ya yi a tsakanin ‘yan Najeriyar.