1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Habaka dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa

January 21, 2025

Najeriya da Faransa sun bude sabon babi dangantaka inda kasashen guda biyu suka saka hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar da ke shirin habbaka hakar ma'adinai cikin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4pRSh
Ma'adanan Najeriya
Ma'adanan NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

A birnin Riyadh da ke Saudiyya ne dai jami'an kasashen guda biyu suka saka hannu bisa yarjejeniyar da ke zaman ta farko kuma ke shirin kawo sauyi cikin batun ma'adinan Najeriya. Kuma a karkashin sabon tsarin da bangarorin biyu suka fara aiwatarwa a cikin wannan mako dai Faransa na shirin taimakawa Najeriya wajen sabuntar masana'antar da ta dauki lokaci tana tangal-tangal.

Karin Bayani: Tinubu zai kulla alaka da Faransa bayan yankar kaunar AES

Faransa, Najeriya | Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da Shugaba Emmanuel Macron na FaransaHoto: Sarah Meyssonnier/REUTERS

Faransa dai za ta aikawa da Najeriya sunaye na kamfanoni na kasar da ke cikin harkar ma'adinan, ko bayan kudi da fasaha ta zamani. To sai dai sabuwar yarjejeniyar ke shirin jawo takkadama a Najeriyar inda suna da kima ta Faransa ke kara kasa, musamman bayan takun saka da kasashen da ta yi musu mulkin mallaka na yammacin Afirka da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Mali gami da Burkina Faso.

Najeriya dai na akllon shigar kasar ta faransa da idanu na tara dukiya cikin harkar dake iya komawa ta kan gaba wajen batu na arziki a Najeriya. Da kyar da gumin goshi ne dai kasar ta iya samun Naira miliyan dubu 38 a shekarar da ta shude daga ma'adinan maras adadi cikin kasar. Da na sani da ke da zafin gaske, ko kuma neman mafitar rikicin tattali na arziki, an dai tsara kasar ta Faransa za ta sake farfado da ramukan hakar ma'adinan kimanin 2,000 domin cin moriya cikin kasar.

Ya zuwa yanzun ramuka dubu daya kacal ne dai cikin dubu bakwai dake tarayyar najeriyar ke aiki. Abun jira a gani dai na zaman inda take shirin zuwa cikin danyen ganyen a cikin yankin da ke cikin kace nace.