1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran Aschtiani

January 3, 2011

Iran na ci gaba da tsare 'yan jaridar Jamus bisa laifin neman tuntuɓar Sakineh Ashtiani da aka yanke wa hukuncin kisa.

https://p.dw.com/p/zt6G
Sakineh Ashtiani da ɗanta a taron manema labarai.Hoto: AP

A wani taron 'yan jarida da ma'aikatar shari'ar ƙasar Iran ta shirya, Sakineh Asthiani, wadda aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar jefa, ta nemi shigar da ƙarar wasu 'yan jaridar ƙasar nan ta Jamus guda biyu da aka tsare da su a ƙasar ta Iran-abin da ba saban ba ne a wannan kasa.

A ranar 10 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai aka kame' yan jaridar su biyu bayan shigarsu ƙasar da nufin tuntuɓar ɗan Sakineh Ashtiani. Sajjad Kadersadeh. Tun daga wannan lokaci ne kuma mahukuntan ƙasar ta Iran ke tsare da 'yan jaridar biyu bisa lafin shiga ƙasar ba da takardun izini na aikin jarida ba. A ma jiya Lahadi sai da wasu fitattun ƙasar nan ta Jamus suka yi kira da a sake su. Gregor Gysi shugaban masu ra'ayin gurguzu na daga cikinsu.

Ya ce: "Za a iya hana musu shiga ko kuma tilatsa musu ficewa nan take daga ƙasar . Abin da ake magana akai a yanzu shi ne tsare su da aka yi. Ana buƙatar dakatar da haka da kuma nunar da cewa hakan ba zama hanya ce ta gyaran mu'amala ba kuma doka ce kawai za ta yanke hukunci akansu."

A ranar Asabar da ta gabata ne dai aka bai wa Sakineh Asthiani damar fita daga gidan waƙafi domin halartan taron manema labarun da ya samu halartan shugabannin kafafen yaɗa labaru na ƙasashen waje. An gano wannan taro a matsayin wata kafa ta watsa manufofin ma'aikatar shari'ar ƙasar ta Iran. Dalili kenan da ya sa 'yan jarida na ƙasashen ƙetare suka ki su halarci taron. A yayin zaman taron kamfanin dillacin labarun AP yayi wa Sakineh Ashtiani tambaya a dangane da 'yan jaridar guda biyu, inda ya nemi sanin yadda suka shigo ƙasar da kuma yadda suka bayyanar da kansu a matsayinsu na 'yan jarida. Cewa jamusawan biyu su bayyanar da kansu ne a matsyin 'yan jarida a bayyane yake. Kuma tun makonnin da suka gabata ne shugabannin Iran ke amfani da su. A cewar masu sa ido akan al'amuran yau da kullum dai mai yiwuwa ne fitowar Sakineh Asthiani na da alaƙa da wata yarjejrniya da aka cimma tsakaninta da ma'aikatar shari'ar ƙasar ta Iran. Mai yiwuwa ne kuma da wani shiri da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu da ya buƙaci Sakineh Ashtiani ta zargi 'yan jarida biyu domin ta samu wasu damammaki.. Sai da ma aka kame ɗanta bayan da 'yan jarida suka yi yunƙurin yin fira da shi, kafin daga bisani aka sake shi akan beli Kuma mai yiwuwa ne da wani daideto da aka cimma tsakanin ma'aikatar shari'a da lauyoyin Ashtiani ko kafin a sake shi. A dai shekarar 2006 ne aka yanke ma wannan mata hukuncin kisa ta hanyar jefa bisa laifin aikata zina da kuma yi wa mijinta kisa. Bayan da aka nuna adawa da wannan hukuncin daga sassa daban daban na duniya ne dai ma'aikatar shari'ar ta ba da sanarwar dakatar da zartar da hukuncin.

Mina Ahadi ita ce kakakin ƙungiyar da ke yaƙi da hukuncin kisa ta hanyar jefa a nan jamus.

Ta ce:" Gwamnatin islama ta Iran gwamnati ce ta kama karya da ke neman danne hakkin Sakineh Ashtiani da na ɗanta Sajjad. Dalili kenan da ya sa gwamnatin ta Islama ke ɗaukar wannan mataki.

Mawallafi: Steffan Wurzel/Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad TIjani Lawal