Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare da jirage marasa matuka
April 14, 2024Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare 300 da jirage marasa matuka a cikin daren Asabar, to amma Isra'ilan ta samu nasarar kakkabo kusan dukkansu, bisa tallafin Amurka, in ji shugaba Joe Biden na Amurka.
Karin bayani:Sojojin Iran sun kama wani jirgin ruwan kasar Isra'ila a gabar ruwan Gulf
Mr Biden ya sha alwashin kiran taron kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki na duniya, don gudanar da taron gaggawa a Lahadin nan, tare da tattauna hanyoyin bi wajen mayar wa Iran martani, tare da lalubo hanyoyin kwantar da rikicin Gabas ta Tsakiya da ke kara rincabewa.
Karin bayani:Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya
Haka zalika Mr Biden ya kira firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta waya don jaddada masa cikakken goyon bayan Amurka a cikin dukkan lamurransa.
Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari, ya ce hakika Iran ta aikata mummunan laifi, da ka iya jefa yankin cikin tashin hankali.
Harin na Iran dai martani ne ga harin da aka kai wa ofishin jakadancinta na Syria, wanda ya hallaka manyan kwamandojinta.