Sojin Iran sun kama jirgin ruwan Isra'ila a gabar ruwan Gulf
April 13, 2024Jami'an tsaron juyin-juya-hali na Iran sun kama wani jirgin ruwan kasar Isra'ila a gabar ruwan Gulf a Asabar din nan, a daidai lokacin da zaman fargabar rincabewar rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara zafafa, sakamakon ikirarin Iran na yin ramur gayya ga Isra'ila, a dalilin harin da aka kai ofishin jakadancinta na Syria, wanda ya kashe manyan kwamandojinta.
Karin bayani:Kasar Iran ta sha alwashin mayar da martani
Kafar yada labaran Iran IRNA ta ce tuni dakarun gabar ruwan kasar suka karkata akalar jirgin zuwa gabar ruwansu, daga gabar ruwa mai matukar muhimmanci a kasuwancin duniya da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
Karin bayani:Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya
Hukumar kula da hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa ta duniya mai shelkwata a Burtaniya, da kuma wata hukuma da ke kula da tsaron gabar ruwa a duniya Ambrey, sun rawaito cewa dakarun da suka kwaci jirgin ruwan sun yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen durawa kan jirgin, sannan suka kama shi.