Iran ta tura jirgin yaki a tekun Bahr Maliya
January 2, 2024Jirgin ruwan yakin kasar Iran ya shiga tekun Bahr Maliya, a wani yanayi da ke kara tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin Iran din da wasu manyan kasashen duniya.
Ana dai fargabar shigar jirgin yakin a tekun ka iya dagula rikicin Gabas ta Tsakiya musamman wanda ke gudana tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.
Karin Bayani: Biden na sa ran Hamas za ta saki matanen da ta tsare
Tun daga watan Nuwambar da ya gabata, kungiyar Houthi ke tsananta hare-hare kan jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar Suez, a wani mataki na nuna goyon bayanta ga kungiyar Hamas.
Tuni kuma rahotanni suka ce matakin ya tilasta wa jiragen ruwa na dakon kaya zuwa sassan duniya suka rage wucewa ta wannan mashiga. To amma hukumomin Burtaniya sun gargadi Iran da ma kungiyar Houthi cewa wajibi Houthi ta gaggauta dakatar da kaddamar da hari kan jiragen ruwa don guje wa martanin da za ta iya mayarwa kan lamarin.