1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Biden na sa ran Hamas za ta saki matanen da ta tsare

November 20, 2023

Shugaban Amurka ya sanar da cewa an kusa cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas domin ta saki mutanen da ta yi garguwa da su a lokacin da ta kai wa Isra'ila harin bazata.

https://p.dw.com/p/4ZEeY
Biden na sa ran Hamas za ta saki matanen da ta tsareHoto: Israel Defense Forces/Handout/REUTERS

Shugaba Joe Biden ya yi wannan furici ne a yayin wani taron manema labarai da ya gabatar a daura da wasu bukukuwa da aka yi a fadar White House a lokacin da wani dan jarida ya yi masa tambaya kan makomar mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a a harin ranar bakwai da watan Oktoba.

Karin bayani:   Hamas ta sako mutane biyu

A can baya dai shugaban na Amurka ya kawar da duk wani batu yin sulhu da kungiyar Hamas tare kuma da yin buris da kiraye-kiryayen kasashen duniya na a tsagaita buda wuta a Zirin Gaza, wanda dakarun Isra'ila suka yi wa kawanya. 

Karin bayani:  Kasashen Larabwa da na musulmi sun bukaci gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Furucin na mista Biden na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci takwaransa na China Xi Jinping da ya yi amfani da matsayin kasarsa na abokiyar cinakayyar kasashen Larabawa don dawo da kwaciyar hankali da zaman lafiya a yankin.