Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare Rafah
May 11, 2024Duk da gargadin Majalisar Dinkin Duniya cewa za a fuskanci gagarumin bala'i a birnin Rafah mai cunkoson jama'a, dakarun Isra'ila sun kai hare-hare a birnin da ke kan iyakar Masar tare kuma umartar jama'a su fiye daga birnin.
Karin bayani: Mutane fiye da 100,000 sun tsere wa Rafah
Masu aiko da rahotanni da likitoci da ke yankin sun bayar da rahoton kai hare-hare a Arewaci da kuma Kudancin yankunan Falasdinawa, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce an toshe hanyoyin shigar da kayan agaji tun bayan da dakarun Isra'ila suka kutsa gabashin birnin Rafah ta kasa.
Isra'ilar dai ta bijire wa gargadin da kasashen duniya suka yi mata a game da kudirinta na kai farmaki Rafah inda Falasdinawa kusan miliyan daya da rabi ke tsugune cikin mawuyacin hali.
Karin bayani: Amurka ta jaddada adawa da kutsen Isra'ila a Rafah
A daidai wannan lokaci kungiyar Hamas mai iko da Gaza ta wallafa wani faifan bidiyo ta kafar Telegram, inda ta nuna hoton wani dan Isra'ila da ta yi garkuwa da shi a lokacin harin ranar bakwai ga watan Oktoban bara, tare da sakon cewa lokaci na kurewa amma gwamnatinku na nuna halin yaudara.