1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane fiye da 100,000 sun tsere wa Rafah

May 10, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane 100,000 ne suka tsere daga yankin Rafah a cikin kwanaki biyar da suka gabata sakamakon farmakin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa.

https://p.dw.com/p/4fiDh
Mutane na tsere wa birnin Rafah na Zirin Gaza
Hoto: Ali Jadallah/Anadolu/picture alliance

Hankula na kara karkata kan yankin Rafah na Zirin Gaza mai yawan al'ummar da suka kai miliyan daya da rabi sakamakon yadda ake ci gaba da samun dubban Falasdinawa da ke tsere wa sauran sassan Zirin, yayin da yankin na kudancin Gaza ke ci gaba da fuskantar farmakin Isra'ila.

Karin bayani:Isra'ila ta kai hari Rafah duk da gargadin Amirka

Babban jami'in UNICEF a Gaza, Hamish Young ya yi kira da a gaggauta shigar da man fetur da kuma sauran agaji zuwa Zirin mussaman yankin Al-Mawasi da ke zama mafaka ga wadanda suka fice daga birnin Rafa.