Isra'ila na fuskantar matsi daga Amirka kan yakin Lebanon
October 16, 2024An ruwaito cewa, hayaki ya turnuke a birnin Haret Hreit bayan da Isra'ila ta kai farmakin jim kadan bayan da dakarun soji sun bukaci mazauna yankin da su kaura. Isra'ilar ta yi ikrarin lalata ma'ajiyar makaman mayakan Hezbollah. Netanyahu ya sha alwashi ci gaba da yakar kungiyar Hezbollah ne yayin da Amirka ke kara matsa mata lamba kan yadda Isra'ila ke gudanar da yaki a Lebanon da kuma Gaza, tare da neman shigar da karin kayan agaji zuwa Falasdinu.
Karin bayani: Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a tsakiyar Beirut na Lebanon
Shugaba Joe Biden na Amirka, da gwamnatinsa ce babbar mai bai wa Isra'ila makamai, ya gargadi Isra'ilar da kar ta kuskura ta kai hari kan tashoshin nukiliya da kuma na mai mallakin Iran.
A gefe guda, wani babban jami'in diflomasiyyar Iran ya gargadi babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, cewa a shirye Iran take ta mayar da martani kan Isra'ila da za ta yi nadama idan ta kai mata harin ramuwar gayya.