Isra'ila ta kai hari Rafah duk da gargadin Amirka
May 9, 2024Shugaba Joe Biden na Amurka ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta dakatar da tallafin soja ga hukumomin Tel Aviv, idan har Isra'ila ta kai hari a Rafah.
Kafin harin da aka kaddamar a yammacin nan, jakadan Isra'ila a MDD Gilad Erdan ya nuna damuwaa kan barazanar Shugaba Joe Biden na Amurka na dakatar da tura wa Isra'ilan tallafin makamai idan ta kuskura ta shiga birnin na Rafah.
Mr. Erdan ya ce wadannan kalamai na Shugaba Biden sun yi tsauri musamman ganin yadda shugaban ya jajirce wajen goyon bayansu tun bayan da rikici ya barke a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.
Isara'ila ta yi watsi da kira-kirayen da kasashen duniya ke mata na shiga birnin na Rafah, inda tuni ta tura tankokin yaki tare da kokarin kaddamar da farmaki a kan iyaka, inda ta ce nan ne tungar karshe ta kungiyar Hamas duk da yadda wurin ke cike da Falasdinawa fararen hula.