Isra'ila ta kashe mataimakin shugaban kungiyar Hamas
January 2, 2024Mataimakin shugaban kungiyar Hamas Saleh al-Arouri ya gamu da ajalinsa, a wani harin da Isra'ila ta kai a kusa da birnin Beirut na kasar Lebanon. Wannan dai shi ne karon farko tun bayan fara yakin Gaza, da Isra'ila ta kai hari a babban birnin kasar Labanon. A baya dai, fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da ke kawance da Hamas na takaita ne a kan iyaka da ke kudancin kasar.
Karin bayanZirin Gaza: Mutane na ci gaba da halakai:
Hamas ta tabbatar da wannan kisan, yayin da kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon (ANI) ya ce wasu karin mutane hudu sun mutu a harin da Isra'ila ta kai. Shi dai Saleh al-Arouri, wanda Isra'ila ta zarga da jagorantar hare-hare da dama, an zabe shi ne a matsayin mataimakin shugaban Hamas a 2017. Dama dai ya fita daga gidan yari ne a 2010 bayan da ya shafe kusan shekaru 20 a gidan yarin Isra'ila.
Karin bayani: Gaza: Masar da Qatar na neman a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta
Ita kuwa kungiyar Hamas ta ce a shirya take ta ba da hadin kai wajen kafa gwamnatin Falasdinawa daya tilo a yankin yammacin kogin Jordan da kuma zirin Gaza. Shugaban wannan kungiya Isma'il Haniyeh da kansa ne ya yi wannan bayyani a wani jawabi da aka watsa ta kafar talabijin, inda ya ce sun samu shawarwari da dama game da wannan mataki sakamakon yakin da ake fama da shi a Zirin Gaza.
Karin bayaniShirin wata sabuwar yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Hamas:
Sai dai Haniyeh ya bayyana cewar ba za a sako 'yan Isra'ila da suka yi garkuwa da su a Gaza ba, matikar ba a amince da sharadi da Hamas za ta gindaya ba. Idan za a iya tunawa dai, kungiyar Hamas tana ci gaba da yin garkuwa da mutane 129 daga cikin 250 da ta kama bayan da ta kai wa Isra'ila mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban bara.