Gaza: Isra'ila ta yadda a fara kai agaji
October 19, 2023Bayan hawa kujerar naki da kasarsa ta yi yayin kada kuri'a kan wani kudirin da kasar Brazil ta gabatar ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke kira da a dakatar da bude wuta nan take a Zirin Gazan Falasdinu, shugaban na Amurka Joe Biden da ya kai ziyara Isra'ila don jajantawa da jaddada goyan baya kan matakin ci gaba da daukar fansar da take a Zirin Gaza na yiwa mazaunansa lugudan wuta, biyo bayan mummunan harin da kungiyar Hamas mai iko ta yi kan Isra'ila da ya halaka 'yan kasar kimanin 2000, Bidem din ya ce dola a tausayawa mazauna Zirin Gaza da masifar da kungiyar Hamas ke janyowa ke shafarsu.
Kungiyar Hamas dai ta siffanta matakin shigar da agajin da Amurka ta yi zuwa Gaza da ciyar da ragon layya kafin a yanka shi, a cewar kusa a kungiyar Ismail Haniyeh. Tuni dai kasar Masar ta sanar da bai wa motocin dakon kaya 20 damar shiga Zirin Gazan, sai dai kamar yadda shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ke jaddawa cewa babu batun bai wa mazauna zirin kimanin miliyan biyu da rabi damar ficewa zuwa Masar, wadanda suka kwashe kimanin makwanni biyu a killace ana musu lugudan wutar da ma'aikatar lafiyar Falasdinawa ta ce ya halaka fiye da mutane 3,500 900 daga cikinsu kananan yara. Duk hakan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da shugabannin Kasashen Yamma ke ta rige-rigen zuwa yankin domin yin jaje ga Isra'ila da kuma sharewa Falasdinawa hawaye.