Ja ya zama launin 'yan adawa a Afirka
Launin na jini da alamar fushi, ana yawaita ganinsa a tsakanin 'yan adawa a nahiyar Afirka. 'Yan siyasa da masu fafatuka da ma'aikata da ma dalibai suna fifita kananan riguna da huluna masu launin ja.
Jagora cikin ja
Julius Malema da abokan huldarsa suka kafa jam'iyyar masu ra'ayin gaba dai gaba dai ta Economic Freedom Fighters (EFF) a Afirka ta Kudu, bayan da reshen matasa na jam'iyyar African National Congress (ANC) da ke jan ragamar mulki ya kore su a shekarar 2013. Tuni dai Malema da jam'iyyarsa suka samu goyon baya na daukacin masu rajin kishin Afirka.
Launi na sauyi
Babbar jam'iyyar adawa a Zimbabuwe, Movement for Democratic Change (MDC-T) ta dauki hankali, lokacin da kasar ta fada cikin mummunan rikicin tabarbarewar tattalin arziki da har yanzu ba ta farfado ba. Harafin T a sunanta na nuni da mutumin da ya kafa ta, marigayi Morgan Tsvangirai wanda tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe ta tsare ta kuma ci zarafinsa. A baya-bayan nan an haramta mata yin gangami.
Shugaban unguwar marasa galihu
Bobi Wine shi ne lakabin shugaban jam'iyyar Uganda's People Power Movement, Kyagulanyi Ssetamu Robert. Mashahurin mawaki ne. Shugaban kasar Yuganda da ya dade kan mulki Yoweri Museveni ya haramta sanya jar hular da Bobi Wine da magoya bayansa ke sha'awar amfani da ita. Museveni ya ce jar hular an ware ta ne ga sojojin kasar su kadai.
#BringBackOurGirls
A watan Afrilun 2014, Boko Haram ta yi garkuwa da 'yan mata 'yan makarantar sakandare 276 ta garin Chibok a jihar Bornon Najeriya. Daga baya an saki wasunsu wasu kuma sun gudu, amma har yanzu akwai wasu a hannun kungiyar. Aisha Yusuf daya ce a cikin masu fafatukar sako 'yan matan. Wata yekuwa ta kasa da kasa da ke neman sakin su na amfani da alamomi ciki har da #BringBackOurGirls da #ChibokGirls.
Adawa da magudin zabe
Zargin amfani da wani sinadarin gyara kuskure a kan takardun zabe a zaben shugaban kasar Malawi na watan Mayun 2019, ya janyo fushin jama'a baki daya. Jam'iyyar adawa ta Malawi Congress Party (MCP) da magoya bayanta sun yi ta kira ga shugabar hukumar zaben kasar, Jane Ansah da ta yi murabus.
Kungiyoyin neman watsi da akidun mulkin mallaka
A shekarun baya-bayan nan, an samu bullar kungiyoyi dabam-dabam, wadanda da yawa dalibai ne ke yi musu jagora a jerin zanga-zanga a kan tituna da kuma a Intanet karkashin take kamar: #FeesMustFall ko #RhodesMustFall da #GhandiMustFall, domin yin adawa da mutum mutumi na tun zamanin mulkin mallaka da kuma ra'ayoyi irin na mulkin mallaka.
Launin adawa da cin hanci
Kungiyar Congress of South African Trade Unions (COSATU), tarayyar kungiyoyin kwadago ce a Afirka ta Kudu. A shekarar 1985 aka kafa ta, ita ce kuma mafi girma a tsakanin gamayyar manyan kungiyoyin kwadago uku a kasar. Ta kunshi kungiyoyin kwadago 21, ja ne launin da suke amfani da shi. Sun shirya zanga-zangar kasa baki daya domin nuna adawa da cin hanci da rashawa.
Wani launi ga jama'a
Sanye da jajayen riguna, magoya bayan kungiyar 'yanto kasar Angola wato People's Movement for the Liberation of Angola (MPLA), ko kuma jam'iyyar Labour Party, suna rera wakoki a wani gangamin siyasa a Luanda babban birnin kasar ta Angola.
Launin ja ya mamaye gari
Tun a watan Oktoban 2019 kasar Guinea ta yi ta fama da zanga-zangar adawa da gwamnati, inda masu zanga-zangar ke saka jajayen kaya na launin kawancen masu adawa. 'Yan kasar ta Guinea da dama sun fusata da matakin Shugaba Alpha Conde na yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, domin bayar da damar yin wa'adin mulki na uku.
Launin ja ga juyin-juya hali
Tun gabanin shekarar 1848 ja ya zama launin juyin-juya hali. Hafsoshin soja na Romawa na yi wa jikinsu jan fenti lokacin bikin nasara, yayin da Misirawan zamamin da da 'yan Mayan, ke yi wa fuskokinsu jan fenti lokacin bukukuwa. Sobiet ta karbi tuta mai launin ja bayan juyin-juya halin Bolshevik a 1917, sannan daga bisani China da Vietnam da wasu kasashe masu bin tsarin kwaminisanci suka bi sahu.