Jagoran RSF ya gana da 'yan siyasar Sudan
January 2, 2024Talla
Jagoran mayakan rundunarRSF a Sudan Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya yi wata ganawar sirri da 'yan siyasar kasar a birnin Addis Ababa na Habasha, daidai lokacin da mayakansa ke ci gaba da ikirarin samun galaba a yakin da kasar take ciki na watanni tara.
Karin bayani: Sarkakiya da ke tattare da rikicin Sudan
A hannu guda kuma shugabannin kasashen Yuganda da Habasha da Djibouti duk sun gana da Janar Dagalo wanda ake wa lakabi da Hemedti kuma ke ayyana kansa a matsayin shugaban Sudan wacce rikici ya daidaita mutanenta. Sai dai jagoran sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana ganawar da wadannan kasashe suka yi da Janar Dagalo a matsayin abin da bai dace ba.