'Yan adawa na ci gaba da gangami a Kenya
July 28, 2023Jaridar Süddeutsche Zeitung, ta ce Sojoji sun hambarar da gwamnatin kasar Jamhuriyar Nijar. Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum, yunkurin da kasashen Turai ke yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel ya gamu da cikas. Jaridar ta ce lamarin ya faru bayan da jami'an tsaron fadar shugaban kasar suka kama Bazoum, wanda aka zabe shi a watan Fabrairun sheara ta 2021, yanzu kuma sojojin sun ayyana shi a matsayin hambararren shugaba. Daga karshe rundunar sojan Nijar ta goyi bayan sojojin da suka yi juyin mulkin, ya fito ne daga, Kungiyar ECOWAS, Tarayyar Afirka, Tarayyar Turai da kasar Amirka da kuma gwamnatin Jamus, wacce ke da sojoji kusan 100 a kasar da ke yammacin Afirka, kuma ta sha yin tayin kara hadin gwiwa da sojojin Nijar.
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung da duba wata zanga-zangar adawa da gwamnati da aka yi a Kenya. Inda ta ce shugaban 'yan adawan Kenya na fatan kotun kasa da da ke Hague zai hukunta wadanda suka ci zarafin masu zanga zanga. Raila Odinga na son gabatar da shaidun cin zarafin masu zanga-zangar da ya wuce kima ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya. A Kenya, madugun 'yan adawa Raila Odinga ya zargi 'yan sanda da yin amfani da karfin tuwo a kan masu zanga-zangar zargin da bayar da shawarar yiwuwar kama hanya Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC). A halin yanzu yana tattara shaidun da za a gabatar wa kotu. Madugun 'yan adawa na kasar Kenya na magana ne bisa zanga-zangar da yan adawa suka shirya don yin Allah wadai da tsarin haraji da kuma tsadar rayuwa a kasar. Inda yan sanda suka yi amfani da karfi dun murkushe zanga-zangar.
Sai jaridar Berliner Zeitung, wace ta duba taron kasashen Afirka da Rasha. Inda ta ci gaba da cewa tun lokacin da aka fara kai hare-hare a Ukraine, Rasha na kara neman abokanai a fadin duniya, kuma a halin yanzu tana kokarin karfafa huldar diplomasiyya da tabbatar da tsaro da kasashen Afirka. A wannan makon, shugaban Rasha, Vladimir Putin, ke karbar bakuncin taron kolin Rasha da Afirka tare da kasashe da dama na kungiyar a mahaifarsa ta St. Petersburg. Ta yin hakan, Rasha za ta kara zurfafa dangantakarta da kasashen Afirka, a gefe daya kuma za ta kawar da damuwar da ta haifar musamman a Afirka ta hanyar kawo karshen yarjejeniyar sayar da hatsin Ukraine. "Kasuwanci da saka hannun jari gami da kara yin hadin gwiwa kan matsaloli kamar yaki da samar da abinci, yaki da fatara da kare sauyin yanayin ya kamata a fara duba su, a cewar shugaba Putin na kasar Rasha.
Ita kuwa die tageszeitung jaridar ta yi sharhi ne bisa yan gudun hijira: Inda ta ce Kwale-kwalen 'yan gudun hijira ya nutse a tekun da ke wajen babban birnin Skasar Senegal. Jaridar ta ci gaba da cewa mutane 18 ne suka nutse, uku sun tsira. Jaridar tace a daren ranar litinin dinnan ne wani kwale-kwalen 'yan gudun hijira ya sake nutsewa daga kasar Senegal kafin ma ya isa gabar teku. Masu iya nutsewa cikin ruwa da motocin daukar marasa lafiya sun garzaya zuwa wurin, amma taimako ya makara ga yawancin fasinjojin. Da farko mutane 12 aka ce suka mutu, daga baya aka ce sun kai 15 kai daga karshe ma aka tabbatar cewa bakin hauren 18 ne suka mutu, an kawo 'yan tsiraru zuwa asibitin soja na don yi masu jinya.