Jamhuriyar Somaliland tana zaben majalisar dokoki a yau
September 29, 2005Tun lokacinda yankin ya balle daga kasar Somalia a 1991,wannan zabe shine karo na uku da aka gudanar karkashin inuwar jamiyu da dama kuma na farko na zaben yan majalisun dokokin kasar.
Masu jefa kuri akalla dubu dari takwas suke jefa kuriar ta yau cikin jamaar kasar miliyan uku da dubu dari biyar.
Masu sa ido daga kasashen Afrika ta kudu,Kungiyar Taraiyar Turai da kungiyoyi masu zaman kansu suke sa ido a zaben na yau.
Shugaban jamhuriyar Somaliland,Dahir Riyale Kahin a lokacin da yake jefa tashi kuriar ya baiyanawa manema labarai cewa,yanzu lokaci yayi da zasu nunawa kasashen duniya cewa, kasar a shirye take ta sami yancin cin gashin kanta.
Yace gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka wa jamaar kasar na kaddamar da gwamnati bisa tafarkin demokradiya,yace abinda suke bukata yanzu shine adalci daga kasashen duniya.
An dai girke yan sanda a runfunan zabe yayinda wasu kuma suke sintiri akan tituna domin kare duk wani abu da ka iya tasowa a lokacin wannan zabe,da akeyi mako guda bayan yan sanda sun kai farmaki kan wata maboyar yan kungiyar Alqaeda a babban birnin jamhuriyar wato Hargeisa inda suka tsare wani babban dan kungiyar da ake zargi da laifin shirya wasu hare hare akan shugabanin yankin da kuma baki yan kasar waje.
Wasu masu lura da alamura da ka je su komo sun baiyana cewa,wannan zabe zai taimakawa jamhuriyar Somaliland samun karbuwa a matasayin yantacciyar kasa mai ikon cin gashin kanta,daga kasar Somalia ta ainihi, inda ake ci gaba da samun rikici game da karagar mulkin kasar da zai kawo karshen shekaru 14 na tashe tashen hankula a yankin.
Tunda farko dai kasashen duniya sunyi kunnen uwar shegu da bukatar Somaliland na samun yancin kanta daga Somalia,suna masu shakkun cewa ballewarta daga Somalian zai kara munana halin rashin kwanciyar hankali a yankin na kahon Afrika da ke fama da rikici.
Jamiyar dake mulki UDUB da jamiyun adawa na Solidarity Party da kuma UCID da ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2003,dukkannisu sun amince cewa yanzu lokaci yayi da kasarsu zata samu karbuwa a cikin kasashen duniya,kodayake baya ga wannan batu na samun yanci,jamiyun basu ga maciji da juna.
Hakazalika dukkanin bangarorin kowannensu na ikrarin cewa shine ya taiamaka ballewar yankin daga kasar Somalia a watan mayu na 1991 bayan tunbuke gwamnatin Muhammad Siad Barre da ya sanya kasar cikin rudani tare da kakkafa kungiyoyin tawaye dabam dabam a kasar ta Somalia.
A jiya laraba ne ministan harkokin wajen Somalialand ya zargi Kungiyar Taraiyar Afrika AU da laifin hana ruwa gudu ga hankoronta na samun karbuwa a kasashen duniya.
Karkashin kudirin kungiyar ta AU dai, kowace kasa dake nahiyar ta kasance kamar yadda turawan mulkin mallaka suka shata ta,kodayake jamhuriyar ta Somaliland yantacciyar kasa ce na kwanaki kadan bayan samun yanci a 1960,wanda ministan yace hakan ya bata damar samun yancin kanta karakashin kudurin Kungiyar ta AU.
Sai dai kuma kungiyar tace tana bukatar Somaliland ta kasance bangare na kasar Somalia babba ta kuma amince da kafa gwamnatin taraiya karkashin shugabancin karba karba tsakaninsu.