Jami'an diflomasiyya sun fara ficewa daga Haiti
March 11, 2024A daidai lokacin da tashin hankali na gungiyoyin 'yan daba ke kara kazanta a Port-au-Prince babban birnin Haiti, Amurka ta sanar ta fara kwashe ma'aikantan ofishin jakadancinta daga kasar da ke tsibirin ''Caraibe''.
Kazalika ita ma Jamus ta dauke jakadanta tare da wasu jami'an diflomasiyar kasashen Turai domin nisantasu daga barazanar tashin hankalin da ke kara kamari a anguwanin da ke kusa da ofisoshin jakadancin kasashen katare da ke Port-au-Prince.
A baya-bayan nan dai al'amura na kara rincebewa a Haiti tun bayan saka dokar ta baci sakamakon arangama tsakanin jami'an tsaro da gungun 'yan daba da ke kai hare-hare a wasu muhinman gurare ciki har da fadar shugaban kasa da ofisoshin 'yan sanda da kuma da gidajen yari.
Karin bayani: Blinken ya shawarci Haiti ta kafa gwamnatin rikon kwarya
Duba da wannan barazana, kungiyar kasashen tsibirin Caraibe ta ''Caricom'' ta gayyaci wakilan Amurka da Faransa da Kanada da kuma MDD domin gudanar da taron gaggawa a wannan Litinin a kasar Jamaika.