1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaro a Zamfara: Rijiya ta bayar.....?

November 3, 2020

Jami'an tsaron da ke aikin samar da tsaro a kauyukan jihar Zamfara da ke Najeriya karkashin rundunar hadarin daji, sun koka kan yadda tallafin kudin da jihar ke bayar wa ba ya zuwa gare su.

https://p.dw.com/p/3koJi
Nigeria Maiduguri Militär Sicherheit Anti Boko Haram 2014
Yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na fama da rashin tsaroHoto: picture-alliance/epa

Jami'an rundunar ta hadarin daji, da ke kokarin dakile ayyukan 'yan ta'adda a jihar ta Zamfara, sun yi wannan korafin ne cikin tattaunawarsu da DW. Sun kuma yi zargin cewa tallafin na tsayawa ne kawai a fatar baki. Makudan kudi ne dai gwamnatin jihar Zamfara ke kashewa a kowane wata, domin tallafawa jami'an tsaro ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin al'umma, gudun kar jihar ta sake koma wa shekarun baya, inda kusan kowace rana sai an samu rahoton garkuwa da mutane da zubar da jini a yankunan karkara. To sai dai jami'an tsaron da ke cikin rundunar hadarin daji wace ke yaki da 'yan bindiga sun ce wannan tallafi ba ya zuwa gare su.

Jami'an tsaro fiye da 8000 aka jibge a jihar ta Zamafara. A cikinsu akwai sojoji da 'yan sanda da jami'an tsaron farar hula wato Civil Defence, kuma kawo yanzu duk da cewa ana samun hare-hare jefi-jefi, a cewar gwamnan jihar ta Zamfara Bello Muhammad Matawalle kwalliya ta fara biyan kudin sabulu. Ya nunar da cewa a dangane da haka ne ma gwamnatinsa ba ta kasala wurin tallafawa jami'an tsaron da ke fagen daga, yana mai mamaki a kan rashin isar tallafin gare su.

Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
'Yan bindiga sun addabi yankunan Arewa maso Gabashin NajeriyaHoto: DW/Katrin Gänsler

Yaki da 'yan bindiga a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya abu ne mai matukar hadari, tamkar irin wanda jami'an tsaro ke yi ne a jihohin Arewa maso Gabashin kasar, domin sun sadaukar da rayuwarsu a wurin wannan yaki. Masana tsaro irinsu Major Bashir Galma mai murabus, na ganin wajibi ne gwamnati ta tabbatar tallafin kudi da jihohi ke bayarwa ga jami'an tsaron, na zuwa wurin wadanda ke a fagen daga, domin ci gaba da wanzuwar wannan zargi abu ne mai matukar hadari ga samar da tsaro.

Gwamnan jihar dai ya sha alwashin sanya ido sosai da kuma ci gaba da daukar matakan da suka dace wajen samar da tsaro a yankunan karkarar jihar ta zamfara, duk da yake cewa a gefe guda akwai abin da ke kawo cikas a kokarin jihar na magance matsalar. DW dai ta yi kokarin ji daga jami'ai a shelkwatar tsaron Najeriya domin jin martaninsu kan zargin da kananan jami'an rundunar hadarin daji ke ybi, na makalewar tallafin kudi da gwamnatin jihar Zamfaran ke bayarwa domin samar da tsaro. Sai dai kuma kawo wannan lokacin jami'an ba su kai ga sun tuntubemu ba duk kuwa da alkawarin tuntubar mu da suka yi.