1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaron Najeriya sun cafke Sambo Dasuki

Kamaluddeen SaniDecember 1, 2015

A Najeriya Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS sun kame tsohon mai baiwa shugaban Najeriya shawara a bangaren tsaro Col Sambo Dasuki sakamakon badakalar sawo makami na dala biliyan biyu.

https://p.dw.com/p/1HFLb
Nigeria Sicherheitsberater Sambo Dasuki
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Jami'an na DSS dai sun yiwa Col Dasuki daurin talala har na fiye da makwanni uku duk da umarnin da kotu ta bayar kan tafiya zuwa kasashen waje don neman lafiya.

Tun a kwanakin baya ne dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin a kame Col Dasuki saboda zargin yana da hannu a badakalar kwangilar sawo makamai a kasar, a inda tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya musanta cewa ya bashi izinin bada kwangilar.

Tuni dai Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kame tsohon minista a ma'aikatar kudi Mallam Bashir Yuguda da ma wasu jami'ai da dama.