APC ta nada Sanata Abdullahi Adamu
March 27, 2022Gwamnan Jihar Jigawa kuma shugaban kwamitin zaben babban taron jam'iyyar Alhaji Badaru Abubakar, ne ya sanar da sunan Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC a wani taron da aka soma tun jiya Asabar ya zuwa safiyar wannan Lahadin, muna tafe da cikakken rahoto bayan labaran duniyan.
Dan shekaru 75, kuma dan majalisar dattawan tarrayar Najeriyar, Adamu da ke zaman shugaba na biyar a shekaru bakwai na jam'iyyar APC dai na da babban aikin jagorantar masu tsintsiyar da kawunansu ke rabe ya zuwa babban zabe na shekarar badi.
Masu tsintsiyar dai sun share tsawon cikin dare suna cashewa a wani abu da ke nuna alamun mantawa da girman rikicin da ke a gabansu da kila kokarin dorawa a cikin neman nasara a zabukan na shekarar badi.
To sai dai kuma duk da karfi na zuciya ta masu tsintsiyar da ke jagorantar harkoki na kasar, cikin rikicin rashin tsaro da karuwar talauci dai, shi kansa shugaban kasar bai boye dimbin matsalar da ke cikin APC a yanzu ba.
Ko bayan Adamu, ta hanyar sulhun jam'iyyar ta APC ta kai ga tabbatar da zaben Emmanuel Okechukwu Joseph a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar a Kudu a yayin kuma da Sanata Abubakar Kyari ya zamo mataimaki na shugaban jam'iyyar na arewa. Sama da wakilai 7,500 ne dai suka taka rawa a cikin babban taron da ke iya bude sabon babi ga makomar jam'iyyar a nan gaba.