1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar jam'iyyar APC mai mulki a Kano

Nasir Salisu Zango LMJ
February 8, 2022

Har yanzu dai jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano da ke Najeriya, na ci gaba da fama da rikicin cikin gida wanda masana ke hasashen zai iya dusashe nasararta a zabukan da ake tunkara.

https://p.dw.com/p/46gzi
Najeriya I Jam'iyyar APC mai mulki
Ba dai a matakin jiha kadai jam'iyyar ta APC ke fama da rikici ba, har da matakin kasaHoto: DW/K. Gänsler

Yanzu haka dai rikicin na jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriyar da kuma jihar ta Kano, ya bude wani shafi na kace-nace a tsakanin mabiya da 'yan hamayyar jamiyyar. Koda yake kwamitin riko na jamiyyar a matakin kasa ya zartas da hukuncin da yake fatan zai kawo karshen matsalolin jamiyyar a Kano, sai dai masana da dama na hasashen cewar idan har ba an yi da gaske ba rikicin zai iya tagayyara jam'iyyar tare da durkusar mata da nasarar da take hankoran samu a zabe mai zuwa na badi. Wannan ne yasa uwar jam'iyyar karkashin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ta aike da sakon matakin da ta dauka da zai magance mata wannan matsala, inda cikin kunshin wasikar da jam'iyyar ta aikewa gwamnan Kanon Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kwmaishinan yada labarai Kwamared Muhammad Garba ya wallafa ta bayyana matakai hudu da ta dauka.

Karin Bayani: Jam'iyyar APC ta Najeriya cikin rudani

Mataki na farko dai shi ne, sauke kowa daga mukaminsa tun daga matakin mazabu zuwa jiha. Mataki na biyu kuwa jam'iyyar ta ce kada wani danta ya kuskura ya kuma tsoma baki a sabgar jam'iyyar, a wata karamar hukuma da ba tasa ba. Na uku APC ta umarci a kafa kwamitin masu ruwa da tsaki a kowace karamar hukuma, domin samar da sababbin shugabanni. Kana na hudu an kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin uwar jam'iyyar da kuma matakin jiha, wanda shi ne zai rika karbar rahoton kananan hukumomi. Wannan kwamiti ya kunshi gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin jagora, sai kuma tsohon gwamnan jihar ta Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau da tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle da kuma Sanata Abba Ali.
Baya ga wannan jam'iyyar ta yi wasu kalamai mai kama da dannar kirji, domin kuwa a wata gabar ta bayyana cewa gwamna Ganduje shi ne jagoran jam'iyya, kuma ana karfafarsa da ya yi duk mai yiwuwa wajen hadin kan masu ruwa da tsakinta. Saboda haka ana fatan gwamnan zai tabbatar da adalci da daidaito ga kowane bangare. Mai Mala Buni ya kuma jaddada cewa, adalcin da yake magana bai tsaya iya ga rabon mukaman jam'iyya ba, ana kuma fatan gwamnan ya sasanta da kowa a koma uwa daya uba daya. Da yake bayyana matsayinsu a kan wannan kwarya-kwaryan sulhu, kwamishinan yada labarai Kwamared Muhammad Garba ya ce ai sulhu abu ne mai kyau, kuma ba su taba kaucewa matakansa ba.

Najeriya I Zaben APC I Kano
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

Karin Bayani: Rikicin jam'iyyar APC mai mulkin Najeiya

To amma tsagin 'yan aware na G7 karkashin Sanata Ibrahim Shekarau sun yi watsi da wannan mataki na uwar jam'iyyar ta APC, tare da bayyana takaici kan yadda ta yi watsi da matakan da aka dauko wanda tun farko. Alhaji Shehu Dalhatu guda daga cikin 'yan G7 din ya nunar da cewa an sha kiran zaman, sulhu amma sai gwamna ya gagara halarta. Yanzu haka dai 'yan jam'iyyar PDP ta adawa sun fara tunanin samun lagon APC din sakamkon wnanan rikici, inda har ma sakataren yada labarai na jam'iyyar Bashir Sanata ke cewa za ta fadi su kwasa. A hannu guda kuma, ana yin hasashen cewar akwai yiwuwar jam'iyyar PDP tsagin Kwankwasiya ya kafa wata sabuwar jam'iyyar, wacce kuma ake zaton za ta zo daidai lokacin da rikicin cikin gida ke neman kassara APC me mulki. A dangane da haka abin ya zama tamkar bareyi biyu ne ke ta kokawa, gefe kuma ga mayunwacin zaki na jiar.