1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jam'iyyar masu kyamar baki ta yi nasara a zaben Austria

September 29, 2024

Hasashen sakamakon zabe ya nuna jam'iyyar FPO ta samu kashi 29.2% a yayin da OVP kuma ta samu kashi 26.2%.

https://p.dw.com/p/4lDHQ
Jam'iyyar FPO ta samu nasara ne da karamin rinjaye a zaben.
Jam'iyyar FPO ta samu nasara ne da karamin rinjaye a zaben. Hoto: dts Nachrichtenagentur/IMAGO

Shugaban masu ra'ayin rikau na kasar Austria Karl Nehammer ya amince da shan kaye da jam'iyyarsa ta Peoples Party ta yi a hannun jam'iyyar masu matsanancin ra'ayin kyamar baki ta Freedom Party a zaben kasar.

Nehammer ya amince da shan kasa ne bayan da hasashen sakamakon zabe ya nuna jam'iyarsa ta gagara kamo ta FPO a zabukan na majalisu.

Karin bayani: An bude rumfunan zabe mai cike da tarihi a Austria

Da ya ke jawabi ga dandazon magoya bayansa, Mista Nehammer ya ce jam'iyyarsu ta OVP za ta mutunta alkawarin da ta dauka tun kafun gudanar da zaben.

Ko da ya ke bai yi karin haske ko wannan na nufin jam'iyyar ba za ta shiga gwamnatin hadaka da shugaban masu kyamar baki Herbert Karl ba.

Karin bayani: Austria ta sanar da dokar kulle

Magoya bayan jam'iyyar ta masu kayamar baki sun rika murna da daga tutocin jam'iyyar domin nuna farin ciki da nasarar da suka samu a kan jam'iyyar OVP ta 'yan mazan jiya.