Jamiyyun adawan Jamus sun goyi bayan tallafin Girka
February 27, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ya kamata a dauki shirin tallafin da za'a baiwa Girka da mahimmancin. A wani jawabi da ta gabatar a majalisar dokokin Bundestag a wannan litinin ta kuma yi la'akari da irin hatsarin da bayar da wannan tallafin ke tattare da shi. To sai dai Merkel ta bayyana cewa babu wanda zai iya bada tabbacin cimma nasara dari bisa dari bayan an aiwatar da wannan shiri, to amma abu mai mahimmanci shine za'a tabbatar da dorewar manufofin Turai da ma zamanta tamkar tsintsiya madaurin ki daya, idan har aka tabbatar da darajar takardar kudin ta euro. Shugabar gwamnatin ta kuma yi kira ga Girka da ta zage dantse wajen ganin ta aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata a fuskar gwamnatinta da tattalin arzikinta.
Majalisar ta Bundestag ta nuna goyon bayanta bayan da ta kada kuri'a, to sai dai har yanzu ba'a tantance yawan kudin da Jamus zata fitar ba. Ko da yake ana sa ran nan ba da dadewa ba za'a yanke shawarar kan yawan kudin, kasancewar jamiyyun adawa na SPD da Grüner sun bada goyon bayansu ga shirin tallafin.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Usman Shehu Usman