1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dambarwa ta kunno kai a jam'iyyar PDP

August 12, 2022

A cigaba da dambarwar rikici da ya dabaibaye babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeiya, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya nemi kotu ta ayyana shi dan takarar jam'iyyar na halas.

https://p.dw.com/p/4FTpO
Nigeria Atiku Abubakar neuer Präsidentschaftskandidat
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Wiken da ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar na watan yunin da ya shude, yace an tafka kuskure bisa yadda gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya ayyana sauka daga takarar shugaban kasar a zauren babban taron jam'iyyar na kasa. A saboda haka kuma a ka'ida shine yafi cancanta ya zama dan takara na shugaban kasar a zaben na 2023.

Sabon matakin na Wike dai na zaman alamun karshen wani kokari na suhunta tsakanin bangarorin guda biyu da suka dauki lokaci suna musayar yawu bisa yadda dan takarar jam'iyyar Atiku Abubakar ya kau da kai daga Wiken ya kuma kare da Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.

Nigeria PDP Vizepräsident Kandidat Iyorchia Ayu
Hoto: PDP/Facebook

Farin jini cikin jam'iyya, ko kuma gaza hakuri da kaddara, cacar baki da kila ma matakan batanci sun yi nisa a tsakanin yayan jam'iyyar dake rabe a tsakanin bangaren Wike da Atiku.

Ko bayan kalaman ba'a isa ba an hango shi kansa Wiken yana cudanya da 'ya'yan Jami'yyar APC mai mulki a kasar a wani abun dake neman aike sako ga bangaren Atiku, a yayin kuma da Atikun yayi nasarar tunzura wasu a cikin magoya bayan Wike zuwa ga neman bore da kila ma raba kan jam'iyyar PDP reshen jihar Rivers da Wiken ke takama da shi.

Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP
Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDPHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Senata ibrahim kazaure na zaman tsohon mataimaki na shugaban jam'iyyar reshen arewa maso yammacin kasar da kuma ke zargin wasu jiga jigan jam'iyyar da haddasa fitinar.

Akwai dai tsoron cigaban rikicin na iya kaiwa ga hargitsa lamura a cikin jam'iyyar da ta share shekaru takwas tana adawa kuma ke neman mafita a yanzu.

Dr Faruk BB Faruk mai sharhi kan siyasa yace matakin Wiken bai wuci kokarin fasawa kowa ya rasa a cikin PDP da yayanta ke kirshiwar mulki ba.

A watan Satumba ne dai aka tsara fara yakin neman zabe na shugaban kasar. Kuma tuni masu tsintsiyar kasar dake kan mulki suka samar da majalisar yakin zaben a yayin da kuma da lemar ke neman hujewa a cikin marka marka.