1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Najeriya ta samu agajin Jamus

Uwais Abubakar Idris
April 29, 2020

Gwamnatin kasar Jamus ta bai wa Najeriya da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS  taimako na zunzurutun kudi har Euro miliyan biyar da dubu 500 domin yakar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3bZ3N
Deutschland Angela Merkel und Muhammadu Buhari 2016
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: imago/R. Zoellner

Jamus din dai ta bayyana wannan tallafin ne cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar ya bayar a Abuja, inda sanarwar ta nuna cewa tallafin da aka shigara da shi ta asusun taimakawa domin jin kai, ya nuna ya zuwa yanzu Jamus ta bayar da taimako na Euro miliyan 29 tun daga lokacin da aka samar da asusun a 2017.  

Tallafi daga kungiyoyi da kasashe

Tallafin na Jamus dai na zuwa ne, a daidai lokacin da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ya amince a bai wa Najeriya taimakon gaggawa na dalar Amirka biliyan uku da miliyan 400, domin yaki da annobar ta Coronavirus. Duk da irin matsalar da Jamus din ke fuskanta a kasarta na yaki da cutar ta COVID-19 din, ta yi kokari wajen talafawa Najeriyar, abin da ka iya kara yaukaka dankagantakar da ke tsakanin kasashen biyu da ma ta Jamus din da kungiyar ECOWAS din.

Frankreich Paris - Aliko Dangote
Aliko Dangote ya bayar da tallafiHoto: picture-alliance/dpa/C. Petit Tesson

Duk wannan dai na zuwa ne baya ga gudummawar da Najeriyar ke samu a cikin kasar, a kokarin yi wa matsalar taron dangi. To sai dai 'yan Najeriyar sun fara nuna damuwa a kan kudin da ake samu da ma yadda ya kamata a aiwatar da su domin kaucewa karkatar da su ta wata hanya.

Gwamnati ta yi tsarin da ya dace

Sanata Hadi Sirika da ke zaman ministan kula da harkokin sufurin jiragen sama na kasar, wanda ke cikin kwamitin yaki da annobar cutar ta COVID-19 a kasar, ya bayyana cewa sun yi tsarin da ya dace domin tafiyar da tallafin da suke samu. Alummar kasar dai sun zuba idanu, domin ganin yadda za a yi aiki da wadannan makudan kudi a kasar da cutar ta tona asirin zahirin halin da sashin lafiyarta ke ciki.