Karfafa alakar yammacin Afirka da Jamus
July 16, 2024A wani jawabi da ta yi a Dakar babban birnin Senegal din jim kadan bayan saukarta, ministar harkokin kasashen ketaren ta Jamus Annalena Baerbock ta bayyana cewa: "Matsalar tsaro da kuma ci-gaban wannan yankin, na da alaka ta kut-da-kut da tsaronmu da kuma bunkasarmu. Kalubalen da yankin ke fuskanta da ya hadar da na ta'addanci da gudun hijira da aikata manyan laifuka na hadin gwiwa da aka tsara da fatara, duka na shafar nahiyar Turai."
Ziyarar tata na zuwa ne a daidai lokacin da aka fuskanci juyin mulki a kasashen yankin Sahel da suka hadar da Mali da Chadi da Guinea da Sudan da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar da Kuma Gabon tun daga shekara ta 2020 kawo yanzu. Baerbock za kuma ta ziyarci kasar Côte d'Ivoire, wadda ita ma ke zaman guda daga cikin kasashen yankin yammacin Afirkan da suke karkashin mulkin dimukuradiyya.