1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na taka rawa wajen warware rikicin Gabas ta Tsakiya

September 11, 2011

Ganawar ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle da shugaban palesɗinawa da kuma firaministan Isra'ila, da nufin neman mayar da su a kan teburin shawara.

https://p.dw.com/p/12Wqt
Minista Guido Westerwelle na Jamus da kuma shugaban Isra'ila Shimon PeresHoto: picture-alliance/dpa

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yi Allah wadai da afka ma ofishin jakadancin Isra'ila da masu zanga-zanga suka yi a birnin alƙahira, tare da kiran hukumomin Masar da su sauke nauyin da ya rataya musu a wuya na kare ofishin kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada. Westerwelle ya yi waɗannan kalaman ne gabanin tashinsa i zuwa yankin gabas ta tsakiya a wannan lahadin domin ganawa da shugaban Palesdinawa Mahmoud Abbas da kuma firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Wannan ziyarar ta sa ta zo ne a daidai lokacin da palesɗinawa ke yunƙurin neman cikakken wakilci a Majalisar Ɗinkin Duniya. Kakakin ministan harkokin wajen na Jamus ya bayyana cewar Westerwelle zai yi ƙoƙarin shawon ɓangarorin biyu na yankin gabas ta tsakiya da ke gaba da juna na dawo kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi