Jamus: Sabuwar doka kan bakin haure
June 23, 2023A karkashin sabuwar dokar Jamus ta sassauta matakai na neman aiki da kuma samun takardar izini kawo iyali a kasar daga waje. Sai dai wasu daga cikin sharudan da dokar ta tanada sun hadar da koyon harshen Jamusanci, da lakantar fannin aiki da kuma batun shekaru.
Da yake tsokaci kan sabuwar dokar jim kadan bayan amincewa da ita, ministan tattalin arzikin Jamus Robert Habeck, ya ce karancin ma'aikata a Jamus na daga cikin manyan matsaloli da kasar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai ke fuskanta. Daga bisani ministan ya bayyana dokar a matsayin mafita ga koma bayan da kamfanonin Jamus ke samu sakamakon karancin ma'aikata.
To sai dai yayin kuri'ar amincewa da dokar, jam'iyyun CDU da CSU da AFD sun nuna adawar karara suna masu cewa ma'aikatan na iya amfani da wannan dama domin kawo duk danginsu kasar Jamus. Ita kuwa jam'iyyar adawa ta Die Linke kauracewa zaben ta yi.