1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin rantsar da sabuwar gwamnati

Ramatu Garba Baba
December 8, 2021

A wannan Laraba za a rantsar da Olaf Scholz na jam'iyyar SPD a matsayin shugaban gwamnatin Jamus bayan majalisar dokokin Bundestag ta amince da shi da ministocinsa a Berlin.

https://p.dw.com/p/43yac
Olaf Scholz
Hoto: Janine Schmitz/photothek/picture alliance

Za a gudanar da bikin rantsar da sabon shugaban da zai maye gurbin Angela Merkel da ta shafe akalla shekaru goma sha shida a karagar mulki, a hukumance da zarar majalisar dokokin Bundestag ta amince da shi da ministocinsa a Berlin kafin daga bisani shugaban kasa, Frank-Walter Steinmeier ya jagoranci bikin rantsar da shi.

Dan shekaru sittin da uku da haihuwan, ya sha alwashin bin sahun mulkin Merkel a gudanar da shugabanci cikin adalci tare da kara inganta demokradiyyar Jamus a wannan sabon babin da kasar za ta bude in ji zababben shugaban na jam'iyyar SDP mai matsakaicin ra'ayi Scholz.

Daga cikin manufofin sabuwar gwamnatin hadakar da ta hada da, The Green ta masu rajin kare muhalli da FDP masu sassaucin ra'ayi, sun kuduri anniyar aiki tare wajen rage yawan makamashi mai gurbata muhalli da kara albashin ma'aikata da kuma shirin shiga cikin jerin kasashen duniya da suka halasta tabar wiwi.