1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta dakatar da bayar da tallafi ga Falasdinawa

October 10, 2023

Gwamnatin Jamus ta dakatar da dukkanin wani tallafi da ta ke bai wa Falasdinawa sakamakon farmakin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila a karshen makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4XKXG
Ministar kula da tattalin arziki da ci gaban kasa ta Jamus, Svenja Schulze
Ministar kula da tattalin arziki da ci gaban kasa ta Jamus, Svenja SchulzeHoto: Leon Kuegeler/photothek.de/picture alliance

Ministar kula da tattalin arziki da kuma raya kasa ta Jamus, Svenja Schulze ta ce dakatar da tallafin na wucin gadi zai bai wa gwamnatin Berlin isasshen lokacin da za ta tabbatar da cewa ba a karkatar da tallafin ga 'yan kungiyar Hamas ba. Jamus dai na kasancewa daga cikin kasashen da suka fi bai wa yankunan Falasdinawa tallafi.

Karin bayani: Isra'ila ta datse hanyar bayar da ruwan sha ga yankin zirin Gaza 

Tuni da kungiyar Tarayyar Turai da kasar Austria suka sanar da dakatar da tallafin da suke bai wa Falasdinawan na miliyoyin euro domin mayar da martani ga rikici tsakanin dakarun Isra'ila da kuma mayakan Hamas.

Karin bayani: Duniya ta yi kakkausar suka a kan harin Hamas

A share guda, kasashen Jamus da Amirka da Birtaniya da Faransa da kuma Italiya sun sha alwashin bai wa Isra'ila goyon baya na hadin gwiwa sakamakon rikicin da ya barke tsakaninta da Hamas. Shugabannin kasashen biyar dai sun kara jadadda goyon bayansu ne da kuma yin Allah wadai da hari a wani taron hadin gwiwa da suka gudanar.