1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta bude tashar karbar gas ta teku

December 17, 2022

Tuni wani jirgin ruwa dauke da iskar gas ya isa sabuwar tashar ajiyar gas din da ke birnin Wilhelmshaven da ke kusa da teku. Jirgin ruwan da ya fito daga Najeriya na dauke ne da gas din da zai wadaci gidaje 50,000.

https://p.dw.com/p/4L6Qb
Hoto: Michael Sohn/REUTERS

Hukumomin Jamus sun kaddamar da tashar adana makamashin iskar gas din da aka sarrafa, a wani mataki na rayuwa ba tare da makamashin gas na kasar Rasha ba. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ne ya kaddamar da tashar adana gas din na LNG.

Kafin yanzun dai Jamus ba ta da irin wannan tasha ta karbar iskar gas ta teku, inda ta fi samun makamashin ta bututun da ke fitowa daga kasar Rasha. Sai dai rikicin diflomasiyyar da ya biyo bayan yakin Ukraine, yanzu ya sanya mahukuntan Berlin tunanin kara bude wasu karin tashoshin adana iskar gas din baya ga wannan wacce ake budewa a Asabar din nan.