1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta jefa ƙuri'ar ceto kuɗin Euro

September 30, 2011

'Yan majalisar dokokin Jamus sun kaɗa ƙuri'ar da ta kawar da abin da ke kawo cikas a ƙoƙarin ceto kuɗin Euro da kuma tallafa wa ƙasar Girka.

https://p.dw.com/p/12jU3
'Yan majalisar dokokin Bundestag yayin kaɗa ƙuri'ar ceto EuroHoto: dapd

An samu nasarar kawar da duk abin da ke zama karan tsaye ga asusun ceto kuɗin Euro, sakamakon ƙuri'ar da 'yan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag suka kaɗa ba da wani ka ce na ce ba domin ƙara kuɗaden asusun. Wannan nasarar ta samu ne bayan da 'yan majalisar suka kaɗa ƙuri'un amincewa guda 523 bisa 85 na nuna adawa da hakan domin faɗaɗa shirin samar da ɗorewar aikin kuɗi na Tarayyar Turai da kuma manufarsa. Wannan mataki ya kuma ƙara gudunmuwar da Jamus zata bayar zuwa Euro miliyan dubu 211, ko da yake ministan kuɗi Wolfgang Schaueble ya ce babu wani ƙarin kuɗi da gwamnatin Jamus za ta bayar. Wannan labarin dai ya daɗaɗa wa kasuwannin hannayen jari a Turai da Amirka da yake shugabar gwamnatin Jamus ta tsira daga ƙuri'ar da ke zaman zakaran gwajin dafi ga ikonta na siyasa.

A wani ci-gaban kuma jami'an binciken kuɗi na Ƙungiyar Tarayyar Turai da babban bankin Turai da asusun ba da lamuni na duniya sun gana da jami'an gwamnatin Girka a Athens babban birnin ƙasar a matsayin yanki na aikin da suke yi domin bincika yiwuwar ba wa ƙasar ta Girka ƙarin tallafi na Euro miliyan dubu takwas.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal