Jamus ta rufe kananan ofisoshin jakadancin Iran
October 31, 2024Jamus ta dauki matakin rufe kanana ofisoshin jadancin Iran guda uku da ke kasarta, a matsayin martani ga hukuncin kisa da Teheran ta zartar wa wani Bajamushe mai asali da Iran mai suna Jamshid Sharmahd a farkon makon nan.
Karin bayani: Zartar da hukuncin kisa a Iran
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ce ta sanar da matakin a yayin wani jawabi da ta gabatar a birnin New York na Amurka wanda aka watsa kai tsaye a kafar talabijin. Kananan ofisoshin da aka rufe sun hadar da na biranen Frankfurt da Munich da kuma Hambourg, kuma matakin zai shafe kai tsaye ma'aikata guda 32 da ke aiki a guraren kamar yadda ma'aitakar harkokin wajen Jamus sanar a wannan Alhamis.
Sai dai Baerbock ta ce ofishin jakadancin Jamus da ke birnin Teheran zai ci gaba da aiki, sannan kuma fadar mulki ta Berlin za ta ci gaba da alakar diflomasiyya da Iran don kare sauran Jamusawan da gwamnatin Iran ke ci gaba da tsarewa ba bisa ka'ida ba.
Karin bayani: Iran ta rufe cibiyar bunkasa harshen Jamusanci a Tehran
Dama dai Jamus ta dade tana gargadin Iran kan cewa kuskuren zartar wa 'yan kasarta hukuncin kisa na iya shafar alakar diflomasiyyar tsakanin kasashen biyu, sai dai amma har kawo yanzu Teheran ba ta yi martani kan wannan mataki ba.