Jamus: takaddama tsakanin CDU da CSU
April 19, 2021Talla
An dai sanya wa'adin jiya Lahadi domin kawo karshen takaddamar kan wanda zai gaji shugabar gwamnatin Angela Merkel nan da watan Satumbar, tsakanin Armin Laschet na jam'iyar CDU da Markus Soeder na jam'iyar CSU.
Yan takarar da magoya bayansu sun fara wannan tattaunawar ce tun a makon da ya gabata, inda aka kyautata zaton kawo karshenta a jiya Lahadi, sai dai abin ya faskara, bayan kwashe sa'oi uku ana murza gashin baki a ginin majalisar dokokin kasar ta Bundestag.